Wani Mahaifi ya kashe ɗansa mai shekara 6 don yin Tsafi a Gombe

Mummunan al’amari ya faru a Ƙaramar Hukumar Kwami, Jihar Gombe, inda ake zargin wani magidanci da jagorantar sacewa da kisan ɗansa mai shekara shida don yin tsafin kuɗi.
Ana zargin mahaifin yaron a matsayin wanda ya jagoranci wannan kisan, kuma yana cikin wadanda suka tsere, yayin da hukumomi ke ci gaba da farautar sa.
Rundunar 'yan sanda ta Gombe ta tabbatar da cafke mutanen takwas a cikin unguwar Bura-Bunga, waɗanda ake zargi da hannu a cikin wannan mummunan aiki.
Kakakin Rundunar ’yan sanda na Jihar Gombe, DSP Buhari Abdullahi, ya bayyana cewa wadanda aka kama sun amsa cewa sun kashe yaron ne bisa umarnin bokaye, waɗanda suka nemi sassan jikin ɗan adam domin yin tsafin kuɗi.
Bincike ya nuna cewa wani mutum mai shekaru 45, wanda ake zargin shi ne shugaban gungun, ya kashe yaron tare da raba sassan jikinsa gida biyu. An jefa ɓangaren sama cikin rijiyar, yayin da aka bai wa abokan laifinsa ɓangaren ƙasa.
Rahotanni sun tabbatar da cewa wasu bokaye biyu ne suka nemi sassan jikin yaron, kuma wani matashi mai shekaru 18 ne ya sace yaron, sannan wani ya haɗa bokayen da su.
Kwamishinan ’yan sanda, CP Bello Yahaya, ya tabbatar da cewa za a gurfanar da duk masu hannu a wannan kisa a gaban kotu. Ya kuma yi kira ga jama’a da su riƙa sa ido, tare da bayar da rahoton duk wani abu mai kama da wannan ga jami’an tsaro.
Rundunar 'yan sanda ta yi alkawarin daukar matakai masu tsauri domin kawo karshen irin wannan mummunan laifi a cikin jihar Gombe.