Bam Ta Kashe Mutane 8 a Borno

Akalla mutane takwas (8) sun rasa rayukansu, yayin da wasu uku suka jikkata, sakamakon fashewar bama-bamai da ake zargin 'yan ta'addan Boko Haram ne suka dasa a karamar hukumar Gamboru Ngala da ke jihar Borno.
Majiyoyi masu tushe sun bayyana cewa lamarin ya faru ne da misalin karfe 11 na safe a ranar Litinin, lokacin da wasu motocin da ke kan hanyarsu daga Rann — hedikwatar karamar hukumar Kala-Balge — zuwa Gamboru Ngala, suka fada cikin bama-baman da aka binne a hanya.
Majiyar ta ce fashewar ta faru ne kusa da kauyen Furunduma, wanda ke da nisan kimanin kilomita 11 daga Rann, tare da bayyana cewa wadanda suka rasa rayukansu sun hada da mata da yara.
Wani jami’in kungiyar ‘Civilian Joint Task Force’ (CJTF) da ya nemi a boye sunansa ya tabbatar da cewa mutane takwas ne suka mutu a wajen fashewar.
Wata majiyar daban ta nuna damuwa cewa adadin wadanda suka mutu na iya karuwa, ganin cewa mata da yara da dama ne ke cikin motocin da lamarin ya rutsa da su.
A halin yanzu, rundunar soji da kuma ‘yan sanda ba su fitar da wata sanarwa dangane da harin ba, har zuwa lokacin hada wannan rahoto.