Rundunar ‘Yan Sandan Bauchi Ta Cafke Wani Mutum Bisa Zargin Safarar Daliba Don Karuwanci

Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Bauchi tayi nasarar cafke wani mutum mai shekaru 26, Mai suna Johnson John, dake da zama a yankin Gwallameji dake cikin garin Bauchi, bisa zargin safarar wata yarinya 'yar shekaru 19, Mai suna Cecelia Cosmos, don yin karuwanci.
A cewar rahoton 'yan sanda, an zargi John da yaudarar Cecelia a ranar 12 ga Afrilu, 2025, ta hanyar yi mata alkawarin samun aiki a Jihar Lagos, amma sai ya yi amfani da ita wajen safarar don karuwanci.
Lamarin ya kai ga hedkwatar 'Yan Sandan ‘E’ Division a ranar 19 ga Afrilu, 2025, bayan mahaifiyar Cecelia, Rhoda Cosmos, daga Unguwan Kusu a Yelwa ta kai rahoton.
A cikin wata sanarwa da aka fitar ranar Juma'a, mai magana da yawun rundunar, CSP Mohammed Wakil, ya bayyana cewa an mika Cecelia ga wata mace da aka sani da suna “Mama,” wacce ta dauke ta zuwa Burkina Faso don karuwanci.
Bayan samun rahoton, kwamishinan ‘yan sanda, CP Sani-Omolori Aliyu, ya umarci DPO na yankin da ya cafke wadanda ake zargi kuma ya ceto yarinyar.