Cibiyar Kiwo Za Ta Jawo Zuba Jari Daga Cikin Gida Da Waje: Gwamnan Bauchi

Cibiyar Kiwo Za Ta Jawo Zuba Jari Daga Cikin Gida Da Waje: Gwamnan Bauchi

Gwabnan Jihar Bauchi, Sanata Bala Mohammed, ya bayyana cikakken yakini cewa Cibiyar Kiwo da ake shirin kafa wa za ta jawo masu zuba jari daga cikin gida da na ƙasashen waje idan aka kammala ta.  

Gwamnan, wanda ya samu wakilcin Kwamishinan Raya Kiwo na Jihar Bauchi, Dr Bala Musa, ya bayyana haka ne a yayin wata ziyarar tantance filin da aka ware domin aikin, mai girman hekta 200, a Rugar Shanu ta Galambi da ke ƙauyen Galambi, karamar hukumar Bauchi.  

A yayin ziyarar, Gwamna Mohammed ya jaddada cewa aikin gina wannan cibiyar zamani zai fara nan ba da jimawa ba, yana mai cewa wannan yana daga cikin matakan da za su kawo ci gaba ga harkar noma da kiwo a jihar Bauchi da Nijeriya baki ɗaya.  

Gwamnan ya bayyana cewa gwamnatin jihar na aiki tare da Ofishin Ƙasa na Tsare-tsare da kuma Bankin Duniya don tabbatar da nasarar aiwatar da aikin. Ya kuma bukaci al'ummomin dake kewaye da wurin su goyi bayan wannan shiri, yana mai cewa cibiyar za ta samar da damammakin ayyukan yi ga matasa da inganta tattalin arzikin yankin.  

A nasa jawabin, Ko'odinatan Aikin L-PRES na Jihar, Alhaji Musa Adamu, wanda Dr Samuel Maina ya wakilta, ya yabawa gwamnatin jihar Bauchi bisa ware hekta 200 na fili domin aikin, yana mai cewa wannan kyakkyawan mataki ba a samu irinsa a wata jiha ba.  

Manajan Janar na Rugar Shanu ta Galambi, Alhaji Ahmed Muhammad, ya jagoranci tawagar a yayin zagayen wurin, inda ya bayyana cewa manoma da ke amfani da wasu sassan filin za a mayar da su zuwa wurare da aka tanada domin su, don tabbatar da cigaban aikin.