Boko Haram sun kashe mutane 7 a wajen jana’iza a Borno

Akalla mutane bakwai (7) sun rasa rayukansu, yayin da wasu da dama suka jikkata sakamakon harin da ake zargin 'yan Boko Haram suka kai wa al'umma a kauyen Kopl da ke karamar hukumar Chibok, a jihar Borno.
Harin ya faru ne da misalin karfe 6 na yamma a ranar Litinin, lokacin da mutane suka hallara domin yin addu’ar karshe ga mamaci da aka rasata a makon da ya gabata. Maharan sun dira a wurin suna harbin mutane babu kakkautawa.
Wannan hari na zuwa ne sa’o’i kadan bayan wani mummunan hari da ya auku a hanyar Gamboru Ngala zuwa Kala Balge, inda daruruwan matafiya suka fada cikin bama-bamai da aka binne a hanya, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar da dama tare da jikkatar wasu.
Shugaban karamar hukumar Chibok, Hon. Modu Mustapha, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce wadanda suka jikkata an garzaya da su Asibitin Gwamnati na Mubi a jihar Adamawa domin samun kulawa. Ya kara da cewa adadin wadanda suka mutu na iya karuwa duba da cewa ana ci gaba da bincike da ceto kafin a yi jana’izar gobe Talata.
Da yake mayar da martani kan wannan sabon yawaitar hare-hare musamman a yankin kudancin Borno, Sanata Ali Ndume ya bayyana halin da ake ciki a matsayin abin tausayi da fargaba, yana mai cewa lamarin ya fi karfin tunanin dan Adam.
Sanatan ya ce ya samu kiran gaggawa daga wani kauye tsakanin karamar hukumar Hawul ta jihar Borno da garin Garkida a jihar Adamawa, inda aka kashe fiye da 'yan banga 10 a wani hari na daban.
“A cikin wata daya da ya gabata, fiye da mutane 100 ne suka rasa rayukansu a hare-hare daban-daban da aka kai cikin tsari a Sabon Gari, Izge, Kirawa, Pulka, Damboa, Chibok, Askira Uba da sauran wurare da dama,” in ji Ndume cikin damuwa.