ISWAP Na Rike Da Kusan Kauyuka 80 a Jihohin Borno, Benue da Filato – Inji CRA

Kungiyar Kare Haƙƙin Kiristoci a Najeriya (CRA) ta bayyana damuwa kan yadda kungiyar ‘yan ta'adda ta Islamic State’s West Africa Province (ISWAP) ke ci gaba da mamaye al’ummomi a Najeriya, inda ta ce kungiyar ta karbe iko da kusan kauyuka 80 a jihohin Borno, Benue da Filato.
A wata sanarwa da CRA ta fitar jiya, wacce Babban Sakataren ta, Rev. Kallamu Musa Dikwa ya sanya wa hannu, kungiyar ta ce tana sanya idanu sosai kan yadda hare-haren ta’addanci ke kara ta’azzara a yankunan, lamarin da ke barazana ga rayuwar Kiristoci da sauran al’ummar Najeriya. CRA ta danganta aukuwar wadannan kashe-kashe da mamayar da ISWAP ta yi wa al’ummomin.
A cikin makonni uku da suka gabata, hare-hare sun kara tsananta a Borno, Benue da Filato, inda mutane da dama suka rasa rayukansu, gidaje suka lalace, kuma dubban jama’a suka rasa matsuguni. CRA ta bayyana cewa yadda hare-haren ke gudana na nuna cewa an tsara su tsaf domin yada tashin hankali, rashin jituwa ta addini da kuma haifar da rikici da rudani.
Kungiyar ta CRA ta ce ta tura jami’anta zuwa jihohin da abin ya shafa domin tattara sahihan bayanai kan irin barnar da aka yi wa al’ummomin Kiristoci a yankunan. Rahoton farko daga binciken ya nuna cewa fiye da kauyuka 80 yanzu suna hannun 'yan bindiga Fulani. CRA ta ce tana ci gaba da tattara bayanai domin fitar da cikakken rahoto kan irin zaluncin da Kiristoci ke fuskanta, musamman a arewacin Najeriya.
Kungiyar ta jinjina wa Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu bisa sabbin umarnin da ya bai wa jami'an tsaro domin ƙara kaimi wajen dakile ayyukan 'yan ta'adda. Duk da haka, CRA ta bukaci cewa kada umarnin ya tsaya a rubuce kawai, sai an tabbatar da aiwatar da shi tare da hukunta duk wani jami’in tsaro da ya gaza, domin zama izina ga wasu.
Sanarwar ta kuma ja kunnen gwamnonin jihohi da su guji siyasantar da kashe-kashen da ake yi, su fuskanci gaskiya su fadi gaskiya ba tare da rufa-rufa ba.