A Nijeriya Akalla mutum miliyan 11 ne ke fama da ciwon siga ba tare da sun sani ba – Inji Likita

A Nijeriya Akalla mutum miliyan 11 ne ke fama da ciwon siga ba tare da sun sani ba – Inji Likita

A Nijeriya Akalla mutum miliyan 11 ne ke fama da ciwon siga ba tare da sun sani ba – Inji Likita

Zubairu Iliyasu, kwararren likita a asibitin koyarwa na Aminu Kano (AKTH), ya bayyana hakan yayin wani taron kungiyar likitocin da suka kware a fannin kula da kwayoyin halitta da aka gudanar a Kano.

Taron, wanda aka mayar da hankali kan "Endocrinology and Public Health," ya hada masana daga sassan Najeriya daban-daban domin tattauna hanyoyin dakile yaduwar ciwon siga da wasu cututtuka marasa yaduwa a Najeriya da Afirka gaba daya.

Shugaban taron, Musa Borodo, ya bukaci gwamnati da ta kara kokari wajen wayar da kan jama’a kan hanyoyin kare kansu daga kamuwa da ciwon siga da kuma matsalar kiba. Haka kuma, ya shawarci gwamnati da ta samar da tsare-tsare da za su rage nauyin kudin magani ga masu fama da wadannan cututtuka.

Borodo ya kara da cewa taron zai samar da dabarun da za su taimaka wajen kara wayar da kan al'umma kan hanyoyin kare kansu daga kamuwa da cutuka.

A nasa bangaren, shugaban kungiyar ACEN, Williams Balogun, ya bukaci gwamnati da sauran masu ruwa da tsaki da su tanadi kudade domin yakar cututtukan da ba sa yaduwa cikin sauki.

Gwamnan jihar Kano, Abba Yusuf, wanda ya kaddamar da taron, ya tabbatar da cewa gwamnatinsa za ta tallafa wa irin wannan kungiya a kokarinta na yaki da cututtuka.