Wani Abu ya Fashe a Kogi mintuna kadan kafin ziyarar Shugaban Kasa Muhammadu Buhari

Wani abun fashewa ya fashe ranar Alhamis a jihar Kogi mintuna kadan kafin shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kaddamar da wani aiki a jihar ta arewa ta tsakiya.
Mazauna yankin sun ce fashewar da ake kyautata zaton bam ce ta haddasa asarar rayukan mutane akalla hudu a gundumar Karaworo da ke karamar hukumar Adavi. Har yanzu ‘yan sanda ba su tabbatar da adadin wadanda suka mutu ba.
Mazauna kusa da wurin da fashewar ta afku sun shaida wa FIKRAH TV cewa fashewar ta auku ne a kusa da kofar shiga fadar sarkin, kimanin mintuna 30 gabanin ziyarar shugaban kasa Muhammadu Buhari a yankin.
Duk da fashewar bom din, Mista Buhari ya yi nasarar kaddamar da asibitin Reference, Okene, wanda bai wuce kilomita daya da fadar sarkin ba.
Sarkin, Ado Ibrahim, wanda yana cikin manyan baki da aka yi wa takardar neman tarbar shugaban kasar, bai halarci taron kaddamar da mai masaukin baki, Gwamna Yahaya Bello ba.
Ohi na Okengwe, Ahmed Tijjani-Muhammed ne ya wakilci sarkin a wajen taron.
Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, William Aya, har yanzu bai amsa kiran waya da kuma sakonnin tes daga wakilinmu ba domin yin tsokaci kan lamarin.
Cikakkun bayanai daga baya…