Sojoji sun cafke kwamandan kungiyar IPOB da ake zargi da kashe Gulak

Sojoji sun cafke kwamandan kungiyar IPOB da ake zargi da kashe Gulak

Rundunar sojin Najeriya ta kama wani mataimakin kwamandan haramtacciyar kungiyar ‘yan awaren Biafra (IPOB) da ake zargi da kashe Ahmed Gulak, mashawarcin tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan kan harkokin siyasa, kamar yadda PRNigeria ta ruwaito.

Wanda ake zargin, Nwagwu Chiwendu, an kama shi ne ranar Talata a yayin binne mahaifinsa a Mbaise a jihar Imo, a kudu maso gabashin Najeriya.

Mista Chiwendu zai kasance babban mai horas da kungiyar ta IPOB a fannin sarrafa makamai, daga baya ya tashi ya zama na biyu a matsayin shugaba a Temple, wanda yanzu shi ne shugaban kungiyar a jihar.

Wanda ake zargin, Mista Chiwendu, an ce ya bar rundunar sojin Najeriya ya koma kungiyar IPOB ta tsagerun, Eastern Security Network (ESN), a ranar 21 ga watan Janairu.

"Ya yi aiki a kan OPHK kuma don haka yana da kwarewar aiki. An kama shi ne a jiya yayin jana’izar mahaifinsa a Mbaise. Yana kai mu sansanin su a daren yau a Obowo.

“Ya amsa laifin kashe Gulak kuma ya tabbatar da cewa sansaninsa ne ke da alhakin yin garkuwa da ‘yan kasashen waje biyu a hanyar Owerri-Okigwe da kuma kashe sufeto ‘yan sanda biyu da ke yi musu rakiya.

“Su ne kuma suka kashe sojojinmu a wuri guda tare da kona mana Hilux a makon jiya. Haka kuma sun taka rawa a harin da aka kai ofishin INEC da ke Owerri. A yanzu haka yana tare da ‘yan sanda,” PRNigeria ta ruwaito wata majiyar soji tana cewa.

Tarihi


Wasu ‘yan bindiga sun harbe Mista Gulak, jigo a jam’iyyar All Progressives Congress mai mulki a Owerri, jihar Imo, a ranar 30 ga Mayu, 2021.

An kai harin ne a lokacin da dan siyasar ke kan hanyarsa ta zuwa filin jirgin sama na Sam Mbakwe, Owerri, kan hanyarsa ta zuwa Abuja.

Daga baya rundunar ‘yan sandan jihar za ta zargi ‘yan kungiyar ta IPOB da reshenta na ‘yan bindiga, ESN da hannu wajen kashe tsohon mashawarcin siyasa.

Kungiyar IPOB dai kungiya ce da ke jagorantar fafutukar neman kafa kasar Biafra mai cin gashin kanta wacce take son a zartas da ita daga yankin Kudu maso Gabas da kuma wasu sassan Kudu-maso-Kuduncin Najeriya.