Hukumar NAFDAC ta yi gargadi game da yin amfani da kayan bleaching da ya wuce kima.

Hukumar NAFDAC ta yi gargadi game da yin amfani da kayan bleaching da ya wuce kima.

Hukumar NAFDAC ta yi gargadi game da yin amfani da kayan bleaching da ya wuce kima.

A cewar shugaban hukumar ta NAFDAC, galibin gidajen SPA da ke cikin biranen kasar nan na da laifin rashin lafiya na hada sinadarai chemical da wasu kayayyakin irin su pawpaw, karas, da sauran su domin yin man jiki don kasuwanci kawai.

Hukumar kula da ingancin abinci da magunguna ta kasa (NAFDAC) ta gargadi ‘yan Najeriya game da amfani da kayan bleaching fiye da kima, tana mai cewa hakan na iya haifar da cutar kansar fata.

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da mai ba wa hukumar shawara kan harkokin yada labarai Olusayo Akintola ya sanya wa hannu, kuma aka rabawa manema labarai a Abuja ranar Lahadi.

A cewar sanarwar, Darakta-Janar na hukumar, Mojisola Adeyeye, farfesa ce ta bayar da wannan shawarar a karshen makon da ya gabata yayin wani taron tattaunawa na kwanaki biyu na manyan jami’an hukumar a Legas.

Misis Adeyeye ta bayyana cewa yin amfani da kayan bleaching na iya haifar da lalacewar gabobi har ma da mutuwa.