Da dumi-dumi: PDP ba za ta iya lashe zaben shugaban kasa ba tare da ni ba, Wike ya yi alfahari

Da dumi-dumi: PDP ba za ta iya lashe zaben shugaban kasa ba tare da ni ba, Wike ya yi alfahari
Gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike, ya bayyana cewa idan ba tare da sa hannun sa da shiga harkokin jam’iyyar PDP ba, jam’iyyar za ta yi kasa a gwiwa wajen neman shugabancin kasar a zaben 2023 mai zuwa.
Gwamna Wike wanda ya yi magana da safiyar Juma’a a wata tattaunawa ta kai tsaye da manema labarai a gidan gwamnati Fatakwal, ya ce shi da tawagarsa sun himmatu wajen yin tasiri a jam’iyyar.
Wike ya ce wasu daga cikin jihohin PDP sun ci zabe ta hanyar tallafin kudi.
“Idan na bar jam’iyyar a yau, PDP ba za ta iya cin zabe ba. Idan gwamnonin PDP biyar suka ce yau za su tafi, mu ba gwamnonin talakawa ba ne, muna da jajircewa da karfi.
“Babu wanda ke son ya ci zabe kuma har yanzu ya ci gaba da yadda suke yi. Na tallafa wa jihohi da dama da kudi domin su ci zabe a baya, wadanda suka hada da Filato, Ondo, Cross Rivers kuma ba za su iya musun hakan ba”.
Cikakkun bayanai na zuwa nan gaba kadan…