Buhari ya gana da shugabannin tsaro a fadar gwamnati

Buhari ya gana da shugabannin tsaro a fadar gwamnati

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya gana da shugabannin tsaro a fadar gwamnati

Taron kwamitin tsaro na kasa (NSC) yana gudana a fadar shugaban kasa dake Abuja tare da shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Wadanda suka halarci taron da aka gudanar a zauren majalisar akwai mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo; Sakataren gwamnatin tarayya (SGF), Mista Boss Mustapha; mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro (NSA), Manjo Janar Babagana Monguno (rtd); da shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa Farfesa Ibrahim Gambari.

Sauran wadanda suka halarci taron akwai Ministan Tsaro, Manjo Janar Bashir Magashi (rtd); Ministan harkokin cikin gida, Rauf Aregbesola; da kuma ministan harkokin ‘yan sanda, Mohammed Maigari Dingyadi.

Babban hafsan tsaron kasa, Janar Lucky Irabor, shine ya jagoranci hafsan hafsoshin, ciki har da babban hafsan sojin kasa, Laftanar Janar Farouk Yahaya; Babban Hafsan Sojin Ruwa, Vice Admiral Awwal Gambo; da Shugaban Hafsan Sojan Sama, Air Marshal Isiaka Oladayo Amao, a wajen taron.

Sauran wadanda suka halarci taron sun hada da Sufeto-Janar na ‘yan sanda, Alkali Baba Usman; Babban Darakta Janar na Hukumar Tsaro ta farin kaya (DSS), Yusuf Bichi; da Darakta-Janar na Hukumar Leken Asiri ta Kasa (NIA), Ahmed Rufa'i Abubakar.