Bai hallata a sayar da wani abu akan farashi da ba a sani ba ko kuma farashin da za a biya cikin wani lokaci da ba a sani ba

Tambaya
Akwai wani mutum da yake da fili, kuma yana buƙatar kuɗi don haka ya so ya sayar. Wani daga cikin danginsa ya zo ya ba shi kudin da yake so a kan cewa wani bangare ne na farashin filin, amma ba su amince da farashin ko lokacin biyan ragowar kudin ba. Hakan ya faru shekara daya da rabi da ta wuce, kuma farashin filaye yana karuwa.
Shin ya kamata a yi la’akari da farashin fili ne a kan farashin da ake yi a halin yanzu ko kuma a yi shi ne a kan farashin a lokacin da aka biya wasu daga cikin farashin a baya?
Amsa
Godiya ta tabbata ga Allah.
Na farko:
Siyar da abu bisa farashin da ba a san shi ba bai hallta ba, saboda yana haɗe da shubuha. Ɗaya daga cikin sharuɗɗan saye da sayarwa akwai sanin farashin abun sayarwa da wadda za'a saya.
Ibn Hazm (Allah Ya yi masa rahama) ya ce a cikin al-Muhalla (7/512):
Ba ya hallata a sayar da wani abu ba tare da sanannen farashi ba, kamar wanda ya sayar da wani abu bisa farashin kasuwa (ba tare da tantance menene ba), kowane irin, ko kuma ba'a san farashinsa halin yanzu. Duk irin wadannan mu’amaloli ba su da inganci, domin mu’amala ne da ke tattare da shubuha da cin dukiyar mutane ba bisa ka’ida ba.
Ad-Dasooqi (Allah ya yi masa rahama) ya ce a cikin Hashiyah (3/15):
Yana da mahimmanci cewa farashin da abin da za a biya ya kamata su kasance masu sayarwa da mai siye su san su, in ba haka ba cinikin ya ɓaci.
Ibn ‘Aabideen (Allah Ya yi masa rahama) ya ce a cikin Hashiyah (4/529):
Ɗaya daga cikin sharadi na kasuwanci shi ne a san adadin da farashin abin da ake sayarwa.
Ibn Uthaimin (rahimahullah) yana cewa:
Idan ba a san farashin ba, hakan yana haifar da koma bayan ciniki, saboda ɗaya daga cikin sharuɗɗan ciniki shine sanin farashin.
Ash-Sharh al-Mumti’ (8/233)
Na biyu:
Hakazalika, cinikin ba ya aiki idan ba a san lokacin biyan kuɗi ba.
An-Nawawi (Allah ya yi masa rahama) ya ce:
Anyi ijma'i gaba daya cewa bai halatta a sayar da wani abu kan farashi (sanannen) da za a biya cikin wani lokaci da ba a sani ba.
Al-Majmuu’ (9/339)
An-Nafraawi al-Maaliki (Allah ya yi masa rahama) ya ce a cikin al-Fawaakih ad-Dawaani (2/80):
Misalin shubuha a cikin kasuwanci shine mutum ya sayi wani abu akan farashi da aka sani amma za a biya idan al’amura suka yi kyau, ko kuma sai kari ya zo. Ma’amalolin da suka shafi shubuha ba su halatta ba, haka nan kuma ba a sayar da wani abu da ba a sani ba, ko tallace-tallacen da ba a san lokacin biya ba, kamar idan mutum ya ce, “Zan sayar da wannan dabbar, kuma za a biya farashi daga ‘ya’yanta, ko lokacin da abubuwa suka yi kyau.
Bisa ga haka:
Siyar da wannan fili ta hanyar da aka bayyana a cikin tambaya, ciniki ne mara inganci, saboda ba a san farashin ba, kuma ba a san lokacin biya na ragowar farashin ba.
Duk bangarorin biyu dole ne su warware ma'amala: dole ne mai siyarwa ya mayar da kuɗin ga mai siye kuma mai siye dole ne ya mayar da ƙasar ga mai siyarwa. Sa'an nan kuma su sake yin ciniki, a kan farashin lokacin, ko duk abin da suka yarda.
Kuma Allah ne Mafi sani.